Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya amince da gina sabbin layin dogo

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da shirin gina hanyoyin jiragen kasa daga Kano zuwa Daura da kuma Kano zuwa Maiduguri.

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya
Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

Ministan sufuri Rotimi Amaechi ya bayyana haka, inda ya ke cewa matakin wani yunkuri ne na Gwamnatin kasar wajen ganin an shawo kan matsalolin sufuri da suka addabi 'yan Najeriya.

Ministan ya kuma ce Buhari ya amince da gina layin dogo daga Port Harcourt zuwa Maiduguri da Makurdi zuwa Jos da Gombe zuwa Yobe zuwa Maiduguri sai kuma Jigawa zuwa Jamhuriyar Nijar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.