Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya gana da shugabannin PDP da APC

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo, sun gana da jagororin jam’iyyun APC da PDP a fadar gwamnatin kasar da ke birnin tarayya Abuja.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da Ahmed Makarfi na PDP
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da Ahmed Makarfi na PDP FEMI ADESINA
Talla

Kamfanin Dillancin Labaran kasar, NAN ya rawaito cewa, ganawar wadda a aka fara ta tun da misalin karfe 11 na safe agogon kasar,  Ahmed Makarfi shugaban jam'iyyar PDP ya jagoranci tawagarsa, John Odigie-Oyegun na jam'iyyar APC kuma ya jagoranci tasa tawagar.

Ana ganin shugabannin na tattaunawa ne kan batutuwan da suka shafi siyasa da zamantakewar al’umma da kuma matsalar furta kalaman nuna kyamatar juna kamar yadda NAN ta yi Karin bayani.

Shugaban Jam’iyyar PDP Ahmed Makarfi yace banbancin siyasa bai hana su yiwa shugaban kasar Muhammadu Buhari addu’ar Allah Ya bashi lafiya ba.

Yayin da yake jawabi wajen  taron, Makarfi yace suna kallon Buhari a matsayin shugaban daukacin 'Yan Najeriya ne ba wai shugaban APC ba.

Makarfi wanda ya yiwa Buhari alkawarin hadin kai, ya ce a matsayin su na 'yan adawa zasu ci gaba da matsin lamba ga gwamnatin wajen ganin ta yiwa jama’ar kasa aiki, musamman yaki da ta’addanci da kuma farfado da tattalin arzikin kasa.

A na shi jawabi shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana ziyar ta su a matsayin wanda ke nuna hadin kan al’ummar Najeriya ba tare da nuna banbancin addini ko kabila ba.

Shugaban ya ce adawa ba wai nuna kiyayya bane sai dai duba hanyoyin da za’a inganta rayuwar al’ummar Najeriya da kuma samar da ci gaba.

Wannan shi ne kusan karon farko da ake gudanar da irin wannan ganawar tun soma mulkin shugaban sama da shekaru biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.