Isa ga babban shafi
Najeriya-Nijar

Buhari ya yabawa shugaban Nijar mai barin gado Mahamadou Issofou

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yabawa shugaban Jamhuriyyar Nijar Mahamadou Issofou da gwamnatinsa saboda bin tanade tanaden kundin tsarin mulkin kasar kamar yadda doka ta tanada a dai dai lokacin da ake shirin gudanar da zaben shugaban kasa zagaye na biyu.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da takwaransa na Nijar Mahamadou Issoufou.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da takwaransa na Nijar Mahamadou Issoufou. REUTERS/Tagaza Djibo
Talla

Yayin da ya karbi tsohon mataimakin shugaban Najeriya Namadi Sambo kuma wakilin kungiyar ECOWAS da ke sanya ido kan zaben, Buhari ya yaba da yadda zaben shugaban kasar zagaye na farko ya gudana, yayinda ya bayyana fatar alheri ga zagaye na biyu da za a yi a karshen wannan mako.

Shugaban Najeriyar ya ce saboda makotakar da ke tsakanin kasashen biyu da kuma muhimmancin Nijar, zaman lafiyar kasar na da matukar tasiri ga Najeriya domin duk abinda ya taba makocin ka, na iya kaiwa gare ka.

Buhari ya bayyana fatar alheri ga wakilin ECOWAS Namadi Sambo wanda zai koma Nijar domin cigaba da sanya ido kan zaben da zai gudana a karshen wannan mako.

Tsohon mataimakin shugaban Najeriyar, Namadi Sambo yace ana cigaba da gudanar da yakin neman zabe cikin kwanciyar hankali, sakamakon sanya hannun da Jam’iyyun siyasar kasar suka yi na gudanar da harkokin su cikin kwanciyar hankali.

A zagaye na farko na zaben, tsohon ministan cikin gida Bazoum Mohammed ya zo na farko da kashi 39.33, yayin da tsohon shugaban kasa Mahamane Ousmane ya samu kasha 17 domin zuwa na biyu.

Yanzu haka Bazoum da Ousmane zasu sake fafata a karshen wannan mako domin samun wanda zai maye gurbin shugaba Mahamane Issofou dake kare wa’adi biyu na shekaru 10.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.