Isa ga babban shafi
Najeriya-Kano

Tsohon mashawarcin gwamnan Kano na tsare a hannun mu - Hukumar DSS

Hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta tabbatar da cewar, tsohon mashawarcin gwamnan Kano kan kafafen watsa labarai Salihu Tanko Yakasai yana tsare a hannun ta.

Salihu Tanko Yakasai, tsohon mashawarcin gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje kan kafafen watsa labarai.
Salihu Tanko Yakasai, tsohon mashawarcin gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje kan kafafen watsa labarai. © Daily Trust
Talla

Tun da yammacin ranar Juma’a aka nemi tsohon na hannun daman gwamnan na Kano Abdullahi Umar Ganduje aka rasa, abinda ya haifar da zulumi kan makomarsa.

Sai dai a daren jiya Asabar, kakakin hukumar DSS Peter Afunanya ya fitar da sanawar dake tabbatar da cewa su ne suka tsare Salihu Tanko Yakasan.

Ana tsaka da laluben inda tsohon mashawarcin kan kafafen watsa labaran ne gwamnan Kano ya kori jami’in sakamakon caccakar da ya yiwa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da kuma jam’iyyar APC a dukkanin matakai, wadanda yace sun gaza wajen magance matsalolin tsaron da suka addabi kasar.

A Juma’ar da ta gabata, yayin bayyana bacin ransa kan sace daliban makarantar Jangebe sama da 300 da ‘yan bindiga suka yi ta shafinsa na twitter, Salihu Tanko Yakasai ya caccaki shugaba Muhammadu Buhari, tare da gwamnonin APC da kuma jam’iyyar APC da cewar sun gaza cika alkawuran da suka daukar wa ‘yan Najeriya a dukkanin matakai.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.