Isa ga babban shafi
Kano-Ilimi

Gwamnatin Kano ta rufe makarantu saboda rashin tsaro

Gwamnatin Jihar Kano da ke Najeriya ta rufe makarantun kwanan da ke jihar biyo bayan ta'asar da 'yan bindiga suka tafka ta sace dalibai mata daga makarantar Jangebe da ke jihar Zamfara

Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje.
Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje. Solacebase
Talla

Gwamnatin  ta sanar da rufe makarantun kwana guda goma da ke kauyukan jihar saboda tabarbarewar al'amuran tsaro, lamarin da ke bai wa 'yan bindiga damar cin karensu babu babbaka a wasu daga cikin jihohin Najeriya.

Kwamishinan Ilimi na jihar Kano Muhammad Sanusi Sa'idu Idu Kiru ya bayyana cew,  makarantun da matakin  ya shafa sun hada da makarantar GASS Albasu da GSS Kafin Mai Yaki da GSS Ajingi  da GGS Sumaila da GGS Kachako da kuma GGSS Jogana.

Sauran makarantun sun hada Maitama Sule Science College Gaya da GGSS Gezawa da GSS Gyartai da ke garin Kunci, sai kuma GSS Karaye.

Sanarwar gwamnatin ta kuma yi kira ga iyaye da su je su kwashe yaransu daga makarantun da matakin  ya shafa domin umarni ne da zai fara aiki nan take.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.