Isa ga babban shafi
Wasanni

Carl Ikeme ya yi ritaya daga kwallo saboda sankaran jini

Mai tsaron ragar najeriya da ke taka leda a Wolverhamptom Wanderers Carl Ikeme ya tabbatar da ajje aikinsa yau din nan sakamakon cutar sankaran jini da ta tsananta masa.

Carl Ikeme wanda ya shafe tsawon rayuwarsa ta kwallo da Club din nasa na Wolverhampton ya ce matakin ya zame masa wajibi don tsira da rayuwarsa.
Carl Ikeme wanda ya shafe tsawon rayuwarsa ta kwallo da Club din nasa na Wolverhampton ya ce matakin ya zame masa wajibi don tsira da rayuwarsa. Action Images / Henry Browne/File Photo
Talla

Ikeme mai shekaru 32 haifaffen Birtaniya wanda tun farko ma sai da aka sanya sunanshi cikin tawagar da za ta wakilci Najeriya a Rasha amma aka cire saboda cutar, ya wallafa a shafin kungiyar ta sa ta Wolves cewa ciwon shi ya kai tsananin da ba zai iya ci gaba da taka leda ba.

Shugaban kungiyar kwallon kafar ta Wolves Jeff Shi, ya ce dan wasan wanda ya ke taka leda a kungiyar tun yana da shekaru 14 a duniya har zuwa yanzu da ya ke da shekaru 32 ya wuce gaban a kira shi dan wasa sai dai dan uwa.

Ikeme ya taka leda a wasanni fiye da 200 da ya kai Club din ga nasara ciki har da wanda ya daga darajarta a wasannin Firimiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.