Isa ga babban shafi
wasanni

Ozil ya daina buga wa Jamus kwallo saboda wariya

Dan wasan Jamus, Mesut Ozil ya sanar da shirinsa na daina buga wa tawagar kasar tamaula, in da ya bayyana matsalar wariyar a matsayin musabbabin caccakar sa kan kashin da Jamus ta sha a gasar cin kofin duniya da aka kammala a Rasha.

Mesut Ozil na cikin damuwa bayan ya gaza kai Jamus ga gaci a gasar cin kofin duniya a Rasha
Mesut Ozil na cikin damuwa bayan ya gaza kai Jamus ga gaci a gasar cin kofin duniya a Rasha REUTERS
Talla

A wata wasika mai shafuka hudu da aka yada a kafafen sada zumunta, Ozil ya ce, "Cikin sosuwar rai da kuma nazari kan abubuwan da suka faru a baya-bayan nan, ba zan ci gaba da buga tamaula a tawagar kwallon kafar Jamus ba, ina jin akwai batun wariya da rashin girmamawa cikin lamarin.”

Baya ga sukar rashin kai Jamus ga gaci a gasar ta cin kofin duniya a Rasha, Ozil ya kuma sha caccaka kan wani hoto da ya dauka da shugaban kasar Turkiya, Recep Tayyip Erdogan a cikin watan Mayun da ya gabata, abin da ya sa wasu ke dika ayar tambaya game da gaskiyarsa ga tawagar kwallon kafar Jamus gabanin gasar duniya a Rasha.

Har ila yau dan wasan mai tushe a Turkiya wanda kuma ke taka leda a Arsenal ya zargi Hukumar Kwallon Kafar Jamus da gazawa wajen ba shi kariya a yayin wannan caccaka da aka yi ta ma sa.

Tuni ministocin Turkiya da suka hada da na shari’a da na wasanni suka jinjina wa Ozil kan wannan matakin da ya dauka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.