Isa ga babban shafi
Wasanni

Pavard ya zura kwallo mafi kyau a Rasha

An zabi kwallon da Benjamin Pavard na Faransa ya jefa a ragar Argentina a matsayin mafi kyau daga cikin jerin kwallaye 169 da aka zura a raga a gasar cin kofin duniya da aka kammala a Rasha.

Benjamin Pavard na murnar kwallon da ya jefa a ragar Argentina
Benjamin Pavard na murnar kwallon da ya jefa a ragar Argentina ©REUTERS/Pilar Olivares
Talla

Pavard ya zarce takwarorinsa wajen samun mafi yawan kuri'un mutane miliyan 3  da suka kada a shafin intanet na Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya, FIFA, in da suka zabi kwallon da ta fi kowacce kyawun ciyuwa.

Dan wasan mai shekaru 22 ya bugi kwallon ne daga neza, in da ta shige can saman sakon ragar Argentina a wasan da Faransa ta yi nasara da kwallaye 4-3.

A cewar Pavard, bai zaci wannan kwallon za ta ciyu haka ba, amma ya yi kokarin dukan ta ne ta kasa-kasa, lura da cewa kwallon ta zo ma sa ne daga sama.

Kwallon da dan wasan tsakiya na Colombia, Juan Quintero ya jefa a ragar Japan, ita ce ta biyu wajen ciyuwa, yayin da Luka Modric ya yi na uku wajen samun kuri'un bisa kwallon da ya jefa a ragar Argentina.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.