Sojin Najeriya ta saki tubabun Mayakan Boko Haram 244
Rundunar sojin Najeriya ta mikawa Gwamnatin jihar Borno mayakan Boko Haram 244 da suka tuba, cikinsu akwai mata 56 da maza 118 sai kuma kananan yara 51.
Wallafawa ranar:
Shugaban rundunar operation lafiya dole a Borno, Manjo Janar Rogers Nicholas, ya ce sun saki mayakan da suka tuba ne karkashin amincewar Babban hafsan sojin kasar Laftanar Janar Tukur Buratai.
Rogers ya ce sun yi bincike da tantace mutane domin tabbatar da cewa babu wata alaka da ta saura tsakaninsu da Boko Haram.
A lokacin karbansu, Gwamnan Jihar Borno Kashim Shettima ya yabi kokarin da sojin Najeriya ke yi a tsawon shekaru 9 domin murkushe mayakan da kuma alkawarta sada tubabun mayakan da iyalansu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu