Isa ga babban shafi
Najeriya-Boko Haram

'Yammatan Chibok sun ki amincewa da komawa gida

Kungiyar Boko Haram a Najeriya ta fitar da wani sabon faifan Bidiyo a yau, inda ta nuna wasu daga cikin sauran ‘yan matan Sakandiren Chibok da take garkuwa da su.A bayanan da ‘yammatan suka gabatar sun nuna rashin amincewarsu da dawowa gaban mahaifansu, duk da kokarin da gwamnatin kasar ke yi wajen ganin ta kubutar da su.

Guda cikin 'yanmatan da ba a bayyana sunanta ba, ta ce basa fatan komawa gaban mahaifansu la'akari da yadda suka karbi akidar Boko Haram kuma suka gamsu da ita.
Guda cikin 'yanmatan da ba a bayyana sunanta ba, ta ce basa fatan komawa gaban mahaifansu la'akari da yadda suka karbi akidar Boko Haram kuma suka gamsu da ita. REUTERS/Zanah Mustapha
Talla

Bidiyon mai tsawon mintuna 22 da kungiyar ta Boko Haram ta fitar, ta nuna guda cikin 'yammatan wadda bata bayyana sunanta ba na cewa bata fatan komawa gaban mahaifanta, hasalima ta karfi akidar Boko Haram.

Sai dai wasu daga cikin iyayen yammatan sun zargi Boko Haram da tilasta musu furta kalaman, inda guda cikin iyayen 'yammatan Mr Ayuba Alamsa ya ce babu yadda za a yi yammatan su furta wadannan kalamai face bisa tilasci.

Haka zalika faifan bidiyon ya kuma nuno matan jami'an 'yansandan nan da kungiyar ta sace a baya, inda suke rokon gwamnati ta yi kokarin ceto su.

Ceto 'yammatan Sakandiren na Chibok na daga cikin alkawurran da shugaban Najeriyar mai ci Muhammadu Buhari ya yiwa 'yan kasar yayin yakin neman zabensa.

Tun a shekarar 2014 kungiyar Boko Haram ta sace 'yammatan su fiye da 200 daga Makarantarsu da ke garin Chibok a Maiduguri.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.