Isa ga babban shafi
Najeriya

Boko Haram: Ba ‘yar Chibok ba ce ta gudo

Gwamnatin Najeriya ta yi amai ta lashe inda ta bayyana cewa yarinyar da ta gudu hannun Boko Haram ba daya daga cikin ‘yan Matan Chibok ba ne da aka sace sama da shekaru uku.

Najeriya ta yi musayar Kwamandojin Boko Haram saboda matan Chibok 82
Najeriya ta yi musayar Kwamandojin Boko Haram saboda matan Chibok 82 REUTERS/Zanah Mustapha
Talla

A wani sakon kar-ta-kwana da Laolu Akande kakakin mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya aikawa kamfanin dillacin labaran Faransa ya ce yarinyar ba ta cikin ‘yan matan makarantar sakandaren garin Chibok da Boko Haram ta sace.

Da farko fadar shugaban kasa ta sanar da cewa yarinyar ‘yar shekaru 15 na daga cikin ‘yan Chibok da aka sace, wadanda sojoji suka tsinta a jeji bayan ta gudu hannun mayakan.

Kungiyar BringBackOurGirls da ke fafutikar ganin an ‘yanto matan ta ce babu sunan yarinyar a jerin sunayen ‘yan Matan Chibok da Boko Haram ke garkuwa da su.

A ranar 14 ga Afrilu ne Boko Haram ta sace daliban makarantar Chibok kimanin 276, yanzu adadin ‘yan matan 106 suka tsira da suka hada 82 da aka yi musayarsu da wasu kwamandojin Boko Haram.

Musayar ‘yan matan dai na ci gaba da janyo cece-kuce a Najeriya, musamman wani hoton bidiyo da biyo baya inda daya daga cikin shugabannin kungiyar ta Boko Haram da ya ci alfarmar ‘yan Matan ya fito yana yin barazanar kaddamar da sabbin hare hare a Abuja.

Amma fadar shugaban kasa ta yi watsi da barazanar, kamar yadda rundunar sojin Najeriya ta ce farfaganda ce kawai ta 'yan ta'adda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.