Rundunar sojin Najeriya ta ceto mutane kusan dubu biyu daga hannun Boko Haram
A cikin makon da ya gabata Rundunar sojin Najeriya ta ce, bayan farmakin da ta kai a kan mayakan Boko Haram a yankin tafkin Chadi, wadanda suka mika wuya da kuma wadanda aka ceto daga hannun ‘yan bindigar sun haura dubu biyu.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Babban kwamandan rundunar da ke yaki da kungiyar ta Boko Haram manjo janar Rogers Nicholas ya bayyana cewa sojojin Najeriya na ci gaba da samun nasara a yakin da sukeyi da yan boko haram.
Manjo janar Rogers Nicholas ya bukaci mazauna yankunan jihar Borno sun bayar da goyan baya zuwa jami’an tsaro a wannan aiki na dawo da tsaro a wadanan yankuna.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu