Sojoji sun yi gargadi bayan harin Boko Haram a Borno
Rundunar Sojin Najeriya ta fitar da sanarwar gargadi bayan harin da mayakan Boko Haram suka kai jiya laraba a jihar Borno tare da sace manyan motocinsu da ke makare da makamai.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Kamar yadda kamfanin dilancin labaran Faransa, AFP, ya rawaito rundunar ta tura sakon kar-ta-kwana ga dukkanin barikoki da shingayen bincike da ke yankuna arewacin kasar inda abin ya faru domin tsananta bincike.
AFP ya ce an sace motoci 2 na makamai da tankokin yaki 2 lokacin da mayakan suka kai harin ba za ta da yammacin jiya laraba a garin Mainok da ke Borno.
Rahotan ya ce anji karar harbe-harbe lokacin da mayakan ke musayar wuta tsakanin su da sojojin da ke samar da tsaro a Yankin.
Akalla mayakan Boko Haram 9 aka kashe a harin da ke kasance irinsa mai karfi a tsawon makonni.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu