Isa ga babban shafi
Najeriya

Shugaba Buhari ya isa jihar Kano

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya isa jihar Kano don fara ziyarar kwanaki biyu daga wannan Laraba, yayin da rahotanni ke cewa, al’amurran kasuwanci sun tsaya cak.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na II a lokacin ziyarar kwanaki biyu a Kano
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na II a lokacin ziyarar kwanaki biyu a Kano rfi hausa/Dandago
Talla

Ana saran shugaba Buhari ya kaddamar da wasu ayyuka na miliyoyin Naira da suka hada da manyan asibitocin gwamnati guda biyu da gadar kasa da kuma tagwayen hanyoyi mai tsawon kilomita 21.1.

Kazalika shugaba Buhari zai jagoranci kafa arsashin ginin shahararren birnin tattalin arziki, sannan kuma zai duba wasu rukunan gidaje dubu 2 da gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta samar.

An dai tanadi matakan tsaro musamman daga filin jiragen sama na Malam Aminu Kano zuwa gidan gwamnati.

Harkokin kasuwaci sun tsaya cak, yayin da aka rufe shaguna da wasu wuraren hada-hadar sana'a.

Jihar Kano ta bada gagarumar gudunmawa wajen zaben Buhari a 2015.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.