Isa ga babban shafi
Najeriya

Gwamnatin Tarraya za ta taimaka don gina kasuwar Sabon Garin Kano

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya kai ziyara yau asabar a jahar kano don jajantawa dubban al’ummar da suka tafka asarar dukiyoyi sanadiyar gobara a kasuwar Sabon gari

Masu aikin kwana-kwana na kokarin kashe gobara a kasuwar Singa
Masu aikin kwana-kwana na kokarin kashe gobara a kasuwar Singa
Talla

Mr Osinbajo ya kuma ce gwamnati Tarraya zata taimaka wajen gina kasuwar Sabon garin tare da tallafawa wadanda al’amarin ya shafa don rage musu asarar da suka yi sakamakon gobarar.

Sai dai kuma rahotanni a jahar na cewa an sami wasu da dama da suka gudanar da zanga-zanga inda suka tarbi mataimakin shugaban kasar da koken halin kunci da suka sami kansu sakamakon wahalar man fetur da rashin wutan lantarki ga kuma karancin kudi a hannun jama’a

Mr Osinbajo dai ya rarrashi masu zanga-zangar inda ya musu jawabi tattausa da cewa gwamanti na sane da wahalhalun jama’a, ya kuma kara da cewa akwai wasu  sabbin shirye shirye na kawo karshen wahalhalun nan da ba jimawa ba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.