Isa ga babban shafi
Najeriya

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa 'yan kasuwa

Gwamnatin Jihar Kano da ke Najeriya ta ce, za ta kaddamar da gidauniyar tallafa wa daruruwan mutanen da suka yi asarar dukiyarsu sakamakon gobarar da aka yi a kasuwar Sabon Gari. 

Gobarar ta haddasa asarar dukiya mai dimbin yawa kuma ita ce mafi muni da aka taba gani a wata kasuwa da ke birnin Kano.
Gobarar ta haddasa asarar dukiya mai dimbin yawa kuma ita ce mafi muni da aka taba gani a wata kasuwa da ke birnin Kano.
Talla

Gwamnatin ta ce, ta na shirin sake gina kasuwar domin dawo da harkokin kasuwanci kamar yadda aka saba.

Gwamnan Jihar ne, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya sanar da haka bayan ya tarbi gwamnonin jihohin Gombe da Kebbi da Niger da Imo da Borno da kuma jigawa da sika kai ma sa ziyarar jaje sakamakon gobarar kuma sun yi alkawarin bayar da tasu gudun mawar.

Rahotanni sun ce, asarar dukiyar da gobarar ta haddasa ta kai ta biliyoyin Naira kuma masu sharhi sun ce, ita ce mafi muni da aka taba gani a wata kasuwa da ke birnin Kano yayin da ta kona shaguna sama da dubu 4.

Wakilinmu na Kano, Abubakar Dan Gambo ya aiko mana da rahoto.

01:38

Rahoto kan tallafa wa 'yan kasuwan sabon gari

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.