Isa ga babban shafi
Kano

Rikicin siyasa ya jikkata mutane 20 a Kano

Wani rikicin siyasa da ya barke tsakanin magoya bayan Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, da kuma Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi sanadin jikkata mutane 20 ciki harda manyan tsofaffin Jami'an gwamnatin jihar.

Tsohon Gwamnan Kano kuma Sanata a yanzu, Rabi'u Musa Kwankwaso da Gwamna mai ci Abdullahi Umar Ganduje.
Tsohon Gwamnan Kano kuma Sanata a yanzu, Rabi'u Musa Kwankwaso da Gwamna mai ci Abdullahi Umar Ganduje. NAIJ Nigeria
Talla

Rikicin wanda ya faru yayin da mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi ke gabatar da hawan Sallah, a ranar Asabar, magoya bayan tsohon Gwmana Rabi’u Musa Kwankwaso sun zargi magoya bayan gwamnan jihar mai ci Abdullahi Ganduje da far musu tare da taimakon 'yan sanda, zargin da yan sandan suka musanta.

Wanna dai ba shi ne karo na farko da ake samun arrangama ba tsakanin bangarorin guda biyu. Wakilinmu daga jihar Kanon, Abubakar Abdukadir Dangambo ya aiko mana da wannan rahoton.

 

01:31

Rikicin siyasa ya jikkata mutane 20 a Kano

Abubakar Dangambo

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.