Najeriya
Kura Ta Lafa A Kano Bayan Hargitsi Tsakanin Kwankwasiya Da Gandujiya
Rahotanni daga jihar Kano a Najeriya na cewa kura ta lafa bayan kazamin yamutsi da aka samu tsakani magoya bayan tsohon Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso da ake kira ‘yan Kwankwasiya da kuma magoya bayan Gwamna mai ci Dr Abdullahi Ganduje da ake kira ‘yan Gandujiya.
Wallafawa ranar:
Talla
Mutane biyu da suka sami munanan raunuka wato tsohon Sakataren Gwamnati karkashin Gwamna Kwankwaso wato Rabiu Bichi da wani kani na tsohon Gwamna mai suna Sani na samun sauki a asibiti.
Majiyoyin samun labarai na cewa jami'an ‘yan sanda na gudanar da cikakken binciken lamarin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu