Isa ga babban shafi
Najeriya-Boko Haram

Mutane 56 sun rasa rayukansu a Madagali

Akalla mutane 56, aka tabbatar da sun rasa rayukansu, yayinda wasu 177 suka samu raunuka, sakamakon fashewar bamabamai a wata kasuwa da ke karamar hukumar Madagali, a jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Karamar hukumar Madagali
Karamar hukumar Madagali
Talla

Kakakin bataliyar rundunar sojin Najeriya ta 28 a Mubi, Manjo Badare Akintoye ne ya tabbatar da wadannan alkalumma, inda ya ce wasu mata ne biyu suka tada bama baman jikinsu a lokaci guda, a sashin da ake saida hatsi, da kuma kayan gwanjo a kasuwar ta Madagali.

Badare ya ce tuni aka bawa wajen da harin ya auku tasro na musamman ta hanyar tura jami’an tsaro domin kare yiwuwar amfani da damar wajen sake kai wani harin.

Tuni dai shugaban Najeriya Muhd Buhari ya aike da sakon ta’aziya ga Iyalan wadanda harin ya ritsa da su, dama al’ummar jihar ta Adamawa.

A baya dai mayakan Boko Haram sun taba kwace iko da Madagali kafin daga bisani sojin Najeriya su kwato garin daga mayakan.

Har yanzu dai babu wanda ya dauki alhakin kai harin. Sai dai hukumomin tsaron kasar na zargin kungiyar Boko Haram da ta yi kaurin suna wajen kai irin wadannan hare-hare.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.