Isa ga babban shafi
Najeriya

Amnesty International ta bukaci dakatar da rushe gidaje a Najeriya

Kungiyar kare hakkin dan’adam ta Amnesty International, ta bukaci gwamnatin Najeriya ta dakatar da rushe karin dubban gidajen da ke gefen ruwa a jihar Legas wadda ke kudancin kasar.

Daya daga cikin yankunan bakin ruwa da gwamnatin Legas ta bada umurnin rushewa, Makoko.
Daya daga cikin yankunan bakin ruwa da gwamnatin Legas ta bada umurnin rushewa, Makoko.
Talla

Rahotanni sun ce kimanin mutane 30,000 da ke zaune a gefen ruwa a jihar sun rasa gidajensu bayan umurnin da gwamnatin jihar ta Legas ta bada na rushe gidajen da ta ce an gina su ba bisa ka’ida ba.

Amnesty International ta ce dole kafin aiwatar da wannan umarni gwamnatin jihar ta samarwa da mutanen wurin tsugunar da su. Amnesty ta kuma ce tilas a binciki dalilin da ya sa jami’an tsaro a Legas din suka yi gaban kansu wajen aiwatar da rushe gidajen, duk da cewa wata kotu a jihar ta haramta hakan har sai ta saurari shari’a.

A martaninta rundunar ‘yan sandan jihar ta musanta rahoton da ke cewa ta cigaba da rushe wasu gidajen a wannnan sati tare cewa bata hannu kan mutuwar wasu mazauna wurin 4 da suka nutse a ruwa, da suka fada cikin ruwa domin tserar da rayukansu, sakamakon bude musu wuta da jami'an tsaro suka yi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.