Isa ga babban shafi
Nigeria

'Yan Sanda a Lagos sun Kubutar da "Yan Mata uku da aka Sace Daga Makaranta

‘Yan Sanda a jihar Legas dake Nigeria sun yi nasarar kubutar da wasu ‘yan mata uku ‘yan makarantar Sakandare na kwana da aka sace su makon jiya.  

Gwamnan jihar Lagos Akinwumi Ambode
Gwamnan jihar Lagos Akinwumi Ambode
Talla

Kakakin ‘Yan Sanda na jihar Legas Dolapo Badmus ta shaidawa kamfanin Dillancin labaran Faransa cewa kafin wayewar gari yau lahadi aka kubutar da ‘yan matan.

‘Yan matan uku na Makarantar Sakandare na Babington Macaulay ne dake yankin Ikorodu.

Babu wasu bayanai gameda ko an biya wasu kudade ne kafin a kubutar da ‘yan matan.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.