Isa ga babban shafi
Nigeria

An kasa sanin gaskiyar yawan kananan Hukumomi dake hannun Boko Haram a Borno Nigeria

Hedkwatan tsaro na Nigeria ta nuna cewa babu gaskiya zancen da ake yi cewa akwai wasu kananan Hukumomi a jihar Borno dake hannun ‘yan kungiyar Boko Haram, kamar yadda wani wakilin majalisar Dattijan kasar ya sanar. 

Gwamnan Jahar Borno Kashim Shettima ya ziyarci wani a Asibitin Maiduguri wanda ya samu rauni a wani harin bom da aka kai a wata kasuwa.
Gwamnan Jahar Borno Kashim Shettima ya ziyarci wani a Asibitin Maiduguri wanda ya samu rauni a wani harin bom da aka kai a wata kasuwa. REUTERS/Stringer
Talla

Sai dai kuma wasu da basa son a fadi sunayensu, wadanda suka fito daga shiyyar  na cewa har yanzu akwai kananan Hukumomi akalla uku dake hannun 'yan kungiyar Boko Haram a arewacin Borno.

Jihar Borno ta kasance ita ce kawaia Nigeria ke makwabtaka da kasashe uku, Niger, Kamaru da Chadi wadanda suke fama da hare-hare daga 'yan kungiyar Boko Haram.

Dan Majalisar Dattijai daga Tsakiyar Borno ya fara cewa akwai kananan Hukumomi dake hannun 'yan kungiyar Boko Haram, yayinda Hedikwatan Sojan kasar ta musanta ikirarin.

Shima dai Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima ya ce babu wata karamar Hukuma dake hannun 'yan kungiyar Boko Haram yanzu haka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.