Isa ga babban shafi
Najeriya

Rashawa: Gwamnatin Najeriya za ta daure alkalai

Gwamnatin Najeriya ta sha alwashin daure alkalan da suka azurta kan su da kudaden cin hanci da rashawa tare da  kwace kadarorinsu da suka saya da kudaden. 

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi alkawarin yaki da ci hanci da rashawa a kasarsa
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi alkawarin yaki da ci hanci da rashawa a kasarsa REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Ministan shari’a Abubakar Malami  ne  ya bayyana haka a birnin Lagos wajen kaddamar da rahotan kungiyar kare hakkin bil-adama ta SERAP, inda ya ke cewa ya zama wajibi alkalai su tsayar da gaskiya a koda yasuhe.

Malami ya ce gwamnatin Muhammadu Buhari za ta yi iya bakin kokarinta dan hukunta duk wani alkali da aka samu da laifin karbar cin hanci ko kuma azurta kan sa ta hanyar da ba ta kamata ba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.