Isa ga babban shafi

Ana samun karuwar sharar na'urorin lantarki a Kamaru duk da dokar gwamnati

Kwararru da ke sa ido kan yadda sharar na’urorin lantarki ke gurbata muhalli, sun koka kan illolin da bolar ke haifarwa a Kamaru, ciki kuwa har da barazana ga lafiyar dan Adam, duk kuwa da dokar yaki da matsalar da gwamnatin kasar ta kafa tun shekaru 10 da suka gabata.

Dagwalon gurbatattun kayakin na'ura.
Dagwalon gurbatattun kayakin na'ura. REUTERS/Nacho Doce
Talla

Tun a shekarar 2011, gwamnatin Kamaru ta kafa sabuwar dokar da ke tabbatar da bin ka'idojin kare muhalli da lafiyar dan Adam yayin zubar da sharar na’urorin lantarki, a dai dai lokacin da a waccan lokaci bincike ya nuna nahiyar Afirka ke kan gaba a duniya wajen zama dandalin zubar da jujin na lantarki a duniya.

Sai dai shekaru 10 bayan kafa dokar kokarin shawo kan matsalar, har yanzu ba ta sauya zani ba a Kamaru domin kuwa a akasarin filayen sharar da ‘yan gwangwan ke bibiya domin tsintar na’urorin da za a iya sake sarrafawa, bai fi a samu kashi 2 zuwa 5 cikin 100 daga cikin ma’aikatan ba, wadanda suke da lasisi ko horon gudanar da aikin.

Didier Yimkoua, shugaban wata kungiya mai yaki da gurbata muhalli da sharar kayayyakin lantarki ke haifarwa, ya ce na’uorin na kunshe da abubuwa masu cutarwa wadanda za su iya haifar da cututtuka ga dan Adam irin su cancer, barazanar da kullum ke karuwa la’akari da ‘yadda ‘yan gwangwan ba sa sanya safar hannu a lokacin da suke bibiyar sharar da suke tsince-tsince a cikinta.

Wani abin damuwa kuma shi ne yadda masu tsintar bolar kayayyakin lantarkin kan fasa na’urorin da suke dauke da sinadaran mercury ko lead, abinda ya sanya su ke jefa al’umma da muhallins cikin hatsarin shakar guba, baya ga tasu rayuwar da tuni ke cikin barazana.

Sai dai da yake an ce mai rai ba ya rasa motsi yanzu haka kungiyar, Solidarite daya daga cikin wadanda doka ta amince da aikinsu na yin gwangwan da kuma sake sarrafa sharar na’urorin lantarki a Kamaru, ta bayyan shirin gina katafariyar cibiyar gudanar da aikin nata a birnin Doula bayan samun filin da girmansa ya kai kadada biyu da rabi, to amma har yanzu babu tallafin kudaden cimma wannan buri.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.