Isa ga babban shafi

Danyen man fetur na gurbata muhalli da kashi 90 a duniya - Bincike

Wani rahoton bincike ya nuna cewa, danyen man fetur ke gurbata muhalli da kashi 90 a yankin gabas ta tskiya da kuma wasu sassa na arewacin Afrika.

Yadda aikin hakar danyen mai ya gurbata muhalli a Ogoniland da ke yankin Niger Delta a Najeriya.
Yadda aikin hakar danyen mai ya gurbata muhalli a Ogoniland da ke yankin Niger Delta a Najeriya. REUTERS/Akintunde Akinleye
Talla

Dama dai Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya  a wannan shekara ta ce, yanki na gabas ta tsakiya da wasu sassan arewacin Afrika na fama da gurbatacciyar iska mafi muni a doran duniya.

An dai jima ana zaton cewa, hamada ce ke hadddasa akasarin gurbacewar muhalli a yankin, ganin yadda fiye da sau 20 ake samun irin wannan gurbacewar muhallin ta hamada a kowacce shekara a yankin.

A shekarar 2017, wasu masu  gudanar da bincike na kasa da kasa sun kewaya gabashin Mediterranean, inda suka ratsa ta mashighin ruwan Suez da wani yankin tekun Gulf, yayin da suka yi amfani da wata na’ura ta musamman wajen tantance ingancin iskar da ake shaka a wannan yankin.

Masu binciken sun gano cewa, mafi akasarin kwayoyin cututtukan da ke ratsawa  cikin kirjin dan adam, ba komai ke haifar da sub a,  face dan adam da kansa ta hanyar amfani da makamashin danyen man fetur da ke gurbata muhalli.

Masu binciken sun ce, matatun man fetur da ake da su a Saudiya da Hadaddiyar Daular Larabawa,  gami da jiragen ruwan dakon kaya da ke zirga-zirga a tekun Maliya da kuma mashigin ruwan Suez, suke kan gaba wajen haddasa gurbacewar muhalli a yankin na gabas ta tsakiya da kuma wani bangare na arewacin Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.