Shiri na musamman a kan ambaliya
Kamar sauran kasashen duniya, nahiyar Afrika na fama da ambaliyar ruwa irin wadda ba ta taba gani ba a tarihi, wadda ta lalata gidaje da gonaki.
Wallafawa ranar:
Ambaliyar ta yi sanadin mutuwar sama da mutane 160 a jihar Jigawa ta Najeriya, da wasu gwammai a karin jihohi 13 da Chadi.
Miliyoyin mutane ne wannan lamari ya shafa kai tsaye ko kuma akasin haka, sakamakon sauyin yanayi.
Menene ya haddasa wannan ambaliyar ruwa? Me zai kasance tasirinsa a kan tattalin arziki, lafiya da noma? Me za mu iya yi a namu matakin don yaki da sauyin yanayi?
Kasashen da suka ci gaba ne ke da alhakin fitar da kashi 80 na gurbatacciyar iska mai lalata muhalli. Ko akwai wata hanya da za a iya bi wajen tafiyar da ayyukan masana’antu a kasashen nan?
Sashen Hausa na RFI zai sadaukar da wani shiri na musamman a yau da maraice, karfe 4 agogon TU da Ghana, ko kuma karfe 5 agogon Najeriya, Nijar Kamaru da Chadi, inda za mu tattauna wannan lamari na ambaliya tare da amsa tambayoyinku. Za kuma mu ba ku damar tofa albarkacin bakinku a kan wannan maudu’i. Kuna iya kama mu a gajeren zango, ko kuma ta manhajar RFI Pure radio.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu