Isa ga babban shafi

Guterres na ziyara a Pakistan don ganin irin bannar da ambaliyar ruwa ta yiwa kasar

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres da ke ziyara a Pakistan yau juma’a don ganewa idonsa irin banner da ambaliyar ruwa ta yi a kasar, ya bukaci duniya ta tallafawa kasar saboda matsanancin halin da ambaliya ta jefa ta.

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gutteres.
Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gutteres. REUTERS/Tiksa Negeri
Talla

Zuwa yanzu kashi 1 bisa 3 na fadin kasar Pakistan na makare da ruwa wanda masana ke alakantawa da sauyin yanayi bayanda aka yi kiyasin ruwan da ya sauka a sassan kasar ya ninka wanda aka saba samu a kowacce damuna da akalla kashi 6.

Gwamnatin Pakistan ta ce yanzu haka ta na bukatar dala biliyan 10 don sake gina yankunan da mummunar ambaliyar ta lallata, adadin da ke matsayin mai matukar wuya ga kasar ta iya tattara dai dai lokacin da abin da al’umma suka fi bukata bai wuce abinci da wurin kwana ba.

A sakon da ya wallafa a Twitter bayan isar shi Pakistan Guterres ya ce yana tare da al’ummar kasar a lokacin da suke halin tsananin bukatar taimako.

Tuni dai kasashen Duniya musamman daga yankin gabas ta tsakiya suka fara aikewa kasar da agajin abinci da magunguna, bayan da ambaliyar ruwan ta kashe mutane fiye da dubu 1 da 300 ta kuma raba miliyoyi da muhallansu baya ga yin awon gaba da gine-gine yankuna da dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.