Isa ga babban shafi

Ambaliya ta rusa dimbim gidaje bayan fashewar madarsar ruwa a Afrika ta Kudu

Adadin mutanen da suka mutu a ambaliyar ruwan Afrika ta kudu, sakamakon fashewar wata madatsar ruwan da ake tonon ma’adinai ya karu, baya ga kwashe gidaje da motoci a tsakiyar Kasar.

Taswirar Afrika ta Kudu.
Taswirar Afrika ta Kudu. AFP
Talla

Hotunan bidiyo daga gidajen talabijin sun nuna irin ta’adin da ruwan yayi na kwashe hanyoyi da gidaje a Jagersfontein, mai nisan kilometre 100 daga lardin birnin Bloemfontein.

Da farko dai hukumomi sun sanar da mutuwar mutane 3 a hadarin, amma daga baya suka ce gawa 1 aka samu, koda yake ba a gama tantance adadin mutanen da suka mutu a iftilain ba.

Gwede Mantashe ministan ma’adinan Kasar Afrika ta Kudu ya ce ana zargin mutane 5 suka mutu a iftila’in,  wasu 4 sun bace yayin da wasu 4 kuma ke kwance a asibiti rai hannun Allah.

A zantawarsa da manema labarai Mantashe, ya ce akalla gidaje 9 ruwan ya kwashe, wasu gidaje 20 na daban kuma suka lalace.

Da farko dai Sanarwar ta ce akalla mutane 40 cikinsu har da wata mata mai dauke da juna biyu ne aka garzaya dasu asibiti domin basu kulawar gaggawa.      

Kawo yanzu dai ana cigaba da gudanar da bincike da kuma ayyukan agaji domin taimakawa wadanda lamarin ya rutsa da su,  kuma tuni aka kwashe mutanen dake rayuwa a wannan yanki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.