Isa ga babban shafi

Mutane 70 ake yi wa kisan gilla kullum a Afrika ta Kudu

Wani bincike a Afirka ta Kudu ya bayyana cewar, a kowacce rana ana yi wa mutane 70 kisan gilla daga watan Janairu zuwa karshen Yunin wannan shekara ta 2022, abin da ya nuna karuwar kisan da kashi 16 da aka gani a shekarar da ta gabata.

Bincike ya nuna cewa, mutane 70 ake yi wa kisan gilla kowacce rana a Afrika ta Kudu
Bincike ya nuna cewa, mutane 70 ake yi wa kisan gilla kowacce rana a Afrika ta Kudu AP - Yeshiel Panchia
Talla

Ministan 'Yan Sandan kasar Bheki Cele ya bayyana cewar rashin fahimtar juna da rikice-rikice da kuma daukar fansa na daga cikin manyan dalilan da ke sanya aikata kisan gillar, sai kuma ayyukan 'Yan Sakai.

Cele ya ce, abin takaici ne yadda adadin mutanen da ake hallakawa ya karu da kashi 16 da rabi a watanni 6 na farkon wannan shekara, kamar yadda alkaluman hukuma suka bayyana.

Ministan ya ce, a shekarar da ta gabata, ana kashe mutane 65 kowacce rana a fadin kasar Afirka ta Kudu tsakanin watan Janairu zuwa Disamba.

A ranar Larabar da ta gabata, jama’a sun yi wa wasu mutane guda 2 da ake zargin 'Yan fashi ne rotse, inda suka kashe su da duwatsu, kafin kona gawarwakinsu a arewacin Yankin Limpopo lokacin da suka yi kokarin garkuwa da wata mata.

Cele ya kuma ce, an samu raguwar masu aikata laifin fyade a cikin watanni 6 da suka gabata na wannan shekara, inda aka samu fyade 9,516, abin da ke nuna samun fyade sama da 100 kowacce rana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.