Kasar Congo ta dage jerin takunkuman hana yaduwar cutar ta Covid-19
Hukumomin Congo sun ba da sanarwa a jiya asabar cewa an kawo sassauci tare da dage jerin takunkuman hana yaduwar cutar ta Covid-19, wacce ta kashe kusan mutane 400 a kasar tsakanin shekarar 2020 zuwa 2022.
Wallafawa ranar:
Kwamitin daidaito da ke yaƙar cutar ta Covid-19 ya yanke shawarar soke dokar ta-baci bangaren kiwon lafiya, wacce aka kaddamar da ita tun a watan Maris na shekara ta 2020, a duk faɗin ƙasar, da kuma ƙarshen sanya kyalen rufe hantsi da baki.
Bugu da kari, ba a bukatar gabatar da sheidar gwajin cewa ba a dauke da kwayar cutar ta Covid 19.
Kwamitin daidaito wanda shugaban kasar Denis Sassou Nguesso ya jagoranta ya yanke shawarar kawo karshen bukatar ma'aikatan lafiya a wasu yankunan kasar ta Congo Brazzaville.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu