Congo Brazzaville na zaben raba gardama
Al’ummar Congo Brazzaville na zaben raba gardama a yau Lahadi faslata kundin tsarin mulki domin amincewa da kudirin shugaban kasar Denis Sassou Nguesso na neman wa’adin shugabanci na uku.
Wallafawa ranar:
An shafe kwanaki ana zanga-zanga a Congo Brazzaville domin nuna adawa da matakin shugaban kasar na yin tazarce.
‘Yan adawa sun ce akalla mutane 20 suka mutu a zanga-zangar.
Shugaba Sassou Nguesso mai shekaru 71 na son ya gyara kundin tsarin mulkin kasar ne domin samun damar tazarce a zaben da da za a gudanar a badi.
A tsarin dokar kasar, an kayyade shekarun dan takarar shugaban kasa zuwa shekaru 70, sannan an kayyade wa’adin shugabanci zuwa biyu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu