‘Yan Sanda sun hallaka masu zanga-zanga a Congo
‘Yan Sanda a Jamhuriyar Demokradiyar Congo sun harbe wasu mutane uku cikin masu zanga-zangar adawa da gwamanatin da suka fantsama a kewayen birnin Kasar.
Wallafawa ranar:
Wani shaidan gani da ido ya bayyana cewa ‘Yan sanda sun bude wuta a kan masu zanga zangar, lamarin da ya yi szanadiyar mutuwar mutanen da ya hada da abokinsa.
Har ila yau mutane 8 sun samu rauni sakamakon rikicin da ya barke tsakanin Jami’an tsaron da masu zanga zangar adawa da yunkurin shugaban kasar, Denis Sassou Nguesso na tsawaita zaman sa a kan karagar mulki bayan ya shafe shekaru da dama a kai.
Wata majiyar kiwon lafiya ta ce, a halin yanzu mutane 7 na kwance a asibitin Makelekele da ke babban birnin kasar ta Jamhuriyar Congo kuma 5 daga cikin su na fama da munanan rauni na harbin bindiga.
A yau ne dai hukumomin kasar suka haramta gudanar da zanga-zangar bayan ‘yan adawa sun bukaci a gudanar da ita .
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu