Congo
Za a yi kuri'ar raba gardama kan sabon kundin tsarin mulki a Congo Brazzaville.
Shugaban Congo Brazaville Denis Sasso Nguesso ya ce za a gudanar da kuri’ar raba gardama a kasar domin canza kundin tsarin mulkin kasar wanda hakan zai ba shi damar sake tsayawa takara a zaben shugabacin kasar.
Wallafawa ranar:
Talla
Nguesso, mai shekaru 72 a duniya, ya share tsawon shekaru 31 kan karagar mulki, kuma ba ya da izinin tsayawa takara a zaben na shekara mai zuwa.
To sai dai masu hamayya da shi a fagen siyasa sun nuna rashin amincewarsu da hakan, yayin da alamu ke nuni da cewa akwai yiyuwar a samu tarzomar nuna adawa da hakan akan titunan kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu