Isa ga babban shafi
Congo-Brazzaville

Gwamnatin kasar Congo-Brazzaville ta ayyana shiga cikin zaman makoki

Kasar Congo Brazaville ta kaddamar da zaman makoki, bayan faruwar hadarin rumbun aje makamai na ranar lahadi a birnin Brazaville, inda sama da mutane 200 suka rasa rayukansu, a yayin da wasu guda 1.300 suka jikkata, tare da raba wasu sama da 500 da mahalansu, kawo yau laraba dai ba a fara aikin warware makamai a barikin ba, al’amarin da ya kawo tsaiko wajen ci gaba da gudanar da ayukan ceto, inda ake kyautata zaton sake samo wasu karin gawawwakin wadanda suka mutu. Bayan ayyana shiga zaman makokin da gwamnati ta yi a jiya talata, a yau an sassauto da tutar kasar, kamar yadda ministan sadarwa haka kuma kakakin gwamnati, Mr Bienvenu Okiemy ya sanar.Wannan hatsari da ya wakana a kasar ta Congo Brazaville a ranar lahadin da ta gabata, sakamakon hadewar wayoyin wutar lantarki, wanda ya haddasa gobara a rumbun aje makaman, ya zama hadarin rumbun makamai mafi muni da aka taba gani a duniya a cikin shekaru 10 da suka gabata. 

Une femme est traitée à l'hôpital central, après une série d'explosions dans le quartier Mpila à Brazzaville, le 5 mars 2012.
Une femme est traitée à l'hôpital central, après une série d'explosions dans le quartier Mpila à Brazzaville, le 5 mars 2012. REUTERS/Jonny Hogg
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.