Isa ga babban shafi
Amurka-Kimiyya

An sami ci gaba wajen kula da masu fama da cutar sankarar jini

Wani binciken da aka gudanar a kasar Amurka ya gano cewa wani maganin da ake yiwa masu fama da cutar sankara ko Cancer, yana karfafa kariyar jikin masu fama da cutar sankarar jini, da aka fi sani da leukemia kan wasu mutane.

Hoton kwayar cutar Cancer
Hoton kwayar cutar Cancer (DR)
Talla

Kwararrun sun bayyana cewa matakin ya sami gagarumar nasara a tsarin, da ake kira immunotherapy a Turance.
Cibiyar yaki da cutar sankara ko Cancer ta jami’ar Pennsylvania ce ta samar da tsarinm da aka fi sani da CTL019, da kuma ke tallafawa jikin bil Adama wajen kashe kwayoyin cutar ta Cancer.
Mujallar kimiyya ta Translational Medicine, tace an yi amfani da wasu marasa lafiya su 14 n e wajen gwajin wannan sabon tsarin a karon farko, inda kuma 8 daga cikin su, wato kashi 57 cikin 100 suka sami sauki gaba daya, yayinda 4 suka sami sauki kadan.
Mutumin da aka fara yiwa magani ya kwashe shekaru 5 ke nan ba tare da alamun cutar Cancer ba, yayinda kuma wasu 2 suka kwashe shekaru 4 da rabi ba tare da alamar cutar ta dawo musu ba.
Wani majinyaci ya kwashe watanni 21 kafin ya mutu, sakamakon kwayoyin cutar da suka shige shi, a yayin tiyatar da aka masa, kan wata cutar da bata da alaka da leukemia.
Wannan sabon binciken ya sanya fatan kawo karshen amfani da magunguna dake cutar da jikin masu fama da Cancer, a lokacin da ake musu magani.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.