Cutar Sankara zata karu kafin 2030
A ranar 4 ga watan Fabrairu ne Majalisar dinkin Duniya ta ware domin yaki da cutar Sankara ko Daji da ake kira Cancer a fadin duniya. A cikin wani Rahoto na Majalisar Dinkin duniya an bayyana cewa za’a samu karuwar masu kamuwa da cutar zuwa shekarar 2030.
Wallafawa ranar:
An bayyana cewa kusan mutane Miliyan takwas ne ke mutuwa da cutar a duk shekara a fadin duniya, kuma sama da ‘yan Najeriya Dubu Dari Biyu da Hamsin ne ke kamuwa da cutar duk shekara, wadda saboda haka ne ake ganin tana sahun gaba a cikin cutuka masu saurin kashe jama’a a fadin duniya duniya.
Wakilinmu RFI Hausa daga Bauchi, a Najeriya Muhammad Ibrahim ya duba mana matsayin cutar a duniya da Najeria a cikin rahoton da ya aiko.
Rahoto: Cutar Sankara zata karu kafin 2030
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu