Isa ga babban shafi
Amurka

An samu sassaucin kisa daga cutar sankara

Wani bincike da kwararru a fannin likitanci suka gudanar na nuna cewa yiwuwar mutuwa daga cutar sankara ko kuma cancer a kasar Amurka ya ragu da kashi ashirin cikin dari. Kungiyar da ke kula da cutar cancer ko kuma sankara ta kasar Amurka, American Cancer Society ce ta fitar da sakamakon binciken, a wani rahoton da ta ke fitarwa na shekara shekara.

Kwayoyin cutar Sankara ko Cancer
Kwayoyin cutar Sankara ko Cancer (DR)
Talla

Rahoton ya yi hasashen za a samu sabbin matsalar cutar ta cancer akalla miliyan daya da dubu dari shida da sittin da biyar, kuma za a samu mace mace sanadiyyar cutar na yawan mutane dubu dari biyar da tamanin da biyar a wannan shekara ta 2014, wanda hakan ya gaza adadin da aka samu a bara.

Kazalika, kungiyar tace a cikin shekaru 20 da suka gabata adadin mace-macen daga wannan cuta ya yi sauki sosai, inda aka kaucewa mutuwar mutane sama da miliyan daya tsakanin shekarar 1991 zuwa 2010.

Cikin nau’ukan cutar, a cewar rahoton, cutar sankarar mama ita ta fi addabar mata, ta huhu kuma ta fi addabar maza, inda aka kara gano cewa cutar ta fi raguwa a tsakanin bakaken fata ‘yan asalin nahiyar Afrika da ke zaune a Amurka.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.