Isa ga babban shafi
Amurka

An gano cewa sinadarin DDT nada alaka da cutar daji sankarar nono

Wani binciken da aka shafe shekaru 50 ana gudanarwa a kan matan kasar Amurka, ya gano cewa wadanda iayaynesu suka mu’amala da sinadarin kashe kwari na DDT fiye da kima lokacin da suke ciki, sun fi kasadar kamuwa da cutar sankara nono.Binciken ya nuna cewa irin wadannan matan suna da kasadar kamuwa da sankarar ko Cancer har sau 4, fiye da wadanda basu yi mu’amala da sinadarin ba.

Sankara, ko Cancer ta Nono
Sankara, ko Cancer ta Nono Getty Images/Image Source
Talla

Binciken da aka shafe shekaru 54 ana gudanarwa, yayi nazari kan wasu mata, da uwayensu suka yi mu’amala da sinadarin na DDT a shekarun 1960, lokacin da ake amfani dashi matuka a Amurka.
Bincike da shine irinsa na farkoda ya nuna alaka ta kai tsaye, tsakanin Cancer ko sankarar nono, da sinadarin na DDT, da aka haramta amfani da shi goman shekaru da suka gabata, a kasashen duniya da dama.
Daya daga cikin kwararrun da suka gudanar da binciken, Barbara Cohn tace an dade ana zargin wasu sinadaran da ake amfani dasu yau da kullum, a matsayin masu sanadiyyar sankarar nono, amma kuma sai yanzu aka sami gamsassun bayanan dake tabbatar da hakan.
Wani binciken da aka yi a baya, ya nuna yadda mu’amala da DDT ke jawo matasloli a halittar yara da ake haifa, raguwar haihuwa da ma ciwon suga da ba na gado ba.
Sai dai duk da haramci daga hukumomi, har yanzu ana amfani da sinadarin na DDT a matuka a wasu kasashen nahiyoyin Africa da Asiya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.