Isa ga babban shafi
Argentina

Kirchner, Shugabar Argentina tana fama da cutar Cancer

Gwamnatin kasar Argentina ta bada sanarwar cewa shugabar kasar Fernandez Kirchner tana fama da cutar Cancer kuma a ranar hudu ga watan Janairu ne za’a yi wa shugabar Tiyata. Kakakin gwamnatin yace shugabar tana fama da cutar cancer ne a makoshinta amma cutar bata yadu a sassan jikinta ba.

Shugabar kasar Argentina Cristina Fernández Kirchner
Shugabar kasar Argentina Cristina Fernández Kirchner Reuters/Martín Acosta
Talla

Uwar gida, Fernandez mai shekaru 58, bata dade da fara shugabancin kasar ba wa’adi na biyu bayan lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar.

A bara ne mijinta tsohon shugaban kasa Nestor Kirchner ya mutu sanadiyar ciwon zuciya.
Yanzu haka shugabar zata mika mulki ga mataimakinta Amado Boudou har zuwa ranar 24 ga watan Janairu tsawon kwanaki 20.

A watan Octoba ne aka sake zaben uwar gida Fernandez wa’adi na biyu bayan samun gagarumin rinjayen kuri’u.

Kusan cutar Cancer ta kasance annoba tsakanin shugabannin kasashen Latin Amurka, domin shugaban kasar Venezuela Hugo Chavez da shugaban Paraguay Fernando Lugo da tsohon shugaban kasar Brazil Luiz Inacio Lula da Silva dukkaninsu sun yi fama da cutar Cancer kafin ayi masu tiyata.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.