Isa ga babban shafi

'Yan sandan Iran sun cafke mayakan ISIS da ke shirin kai hare-hare da Sallah

Jami’an tsaron Iran sun cafke wasu mutane 9 da suka ce ‘ya’yan kungiyar ISIS ne, da suke shirin kai hare-haren ta’addanci yayin bikin Sallah Karama.

Wasu 'yan sandan kasar Iran a birnin Teheran.
Wasu 'yan sandan kasar Iran a birnin Teheran. via REUTERS - WANA NEWS AGENCY
Talla

An cafke maharan ne a lardin Alborz mai nisan kilomita 60 daga birnin Teheran, kamar yadda rundunar ‘yan sandan kasar Iran din ta sanar.

Kamen ya zo ne kasa da watanni hudu, bayan tagwayen hare-haren bam din watan Janairu, da ya lakume rayukan mutane kusan 100, tare da jikkata wasu fiye da 200 yayin taron alhinin tunawa da kisan gillar da Amurka ta yi wa babban kwamandan sojin Iran Qassem Solaimani a birnin Kerman.

Tun a waccan lokacin dai mutane 35 jami’an tsaron na Iran suka cafke bisa tuhumarsu da hannu a munanan hare-haren.

Sa’o’i bayan kai hare-haren ne kuma kungiyar ISIS reshen lardin Khorasan ta dauki alhakinsu, kungiyar da a baya bayan nan ta sake daukar alhakin harin ta’addancin da aka kai kan wani taron kalankkuwar makada a kusa da Moscow, babban birnin Rasha, inda akalla mutane 144 suka rasa rayukansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.