Isa ga babban shafi

Kungiyoyin agaji a Yemen na fargabar tashin wani sabon rikicin a teku

Kungiyoyin bada agaji na kasar Yemen sun koka game da karuwar hare-hare daga bangarori da dama a tekun maliya, dai-dai lokacin da kasashen turai ke harar jiragen yakin Houthi, inda suma suke mayar da martani.

Har yanzu mayakan na kan bakan su na dakatar da duk wani jirgin kaya da zai shiga Isra'ila
Har yanzu mayakan na kan bakan su na dakatar da duk wani jirgin kaya da zai shiga Isra'ila AP - Staff Sgt. Donald Holbert
Talla

Wannan na zuwa ne mako guda bayan da kasashen Amurka da Birtaniya suka yi hadin gwiwa wajen kaddamar da mummunan hari kan jirgin yaki na Houthi da ke kan teku, abinda ke kara rura wutar rikicin gabas ta tsakiya.

Ta cikin watan sanarwar hadin gwiwa da kungiyoyin kimanin 26 suka fitar, sun nuna fargabar tashin wani sabon rikici a Yemen, la’akari da yadda Isra’ila ke yunkurin farmakar mayakan Hamas a cikin kasar, yayin da rashin tsaro ke kara kamari a gabar tekunta.

Sanarwar kungiyoyin ta bukaci majalisar dinkin duniya ta dauki matakin hana tashin wannan rikici, la’akari da hadarin da yake da shi.

Yemen na cikin kasashen da ke fama da matsalolin yaki, a cewar majalisar dinkin duniya abinda ke nufin fiye da kaso biyu cikin uku na yawan al’umar kasar na rayuwa ne kan tallafin da hukumomi, kungiyoyi da kuma kasashe ke basu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.