Isa ga babban shafi

'Yan kasar Indonesiya sun fara kauracewa kayayyakin Amurka da Isra'ila

Hukumar kula da 'yan gudun hijira Falasdinawa ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa za ta dakatar da ayyukanta a Gaza da yaki ya daidaita cikin kwanaki biyu saboda karancin man fetur, yayin da Isa’ila ke ci gaba da luguden wuta a yankin.

Wannan hoton da Dr. Marawan Abu Saada ya fitar ya nuna jariran Falasdinawa bakwaini a asibitin Shifa da ke birnin Gaza a ranar Lahadi, 12 ga watan Nuwamba, 2023.
Wannan hoton da Dr. Marawan Abu Saada ya fitar ya nuna jariran Falasdinawa bakwaini a asibitin Shifa da ke birnin Gaza a ranar Lahadi, 12 ga watan Nuwamba, 2023. AP - Dr. Marawan Abu Saada
Talla

Shugaban hukumar ‘Yan gudun hijara Falasdiwa ta Majalisar Dinkin Duniyar a Gaza Thomas White ya wallafa gargadin ta shafinsa na X da akafi sani da Twitter, inda rashin man fetur zai tilasta musu dakatar da ayyukansu na jinkai a yankin cikin sa'o'I 48, muddun ba’a shigar da makamashin ba.

Motar jami'an agaji na Majalisar Dinkin Duniya a yankin Gaza.25/10/23
Motar jami'an agaji na Majalisar Dinkin Duniya a yankin Gaza.25/10/23 AFP - MAHMUD HAMS

Karancin mai dai ya tilastawa rufe asibitoci a arewacin Gaza yayin da sojojin Isra'ila ke ci gaba da kai hare-hare a cibiyoyin na kiwon lafiya.

Hare-haren Isra'ila

Fiye da Falasdinawa 11,200 ne aka kashe a hare-haren da Isra’ila ke kaiwa zirin Gaza tun ranar 7 ga watan Oktoba.

Ko a Litinin din nan, sama da mutane 30 ne aka kashe a sansanin ‘yan gudun hijira na Jabalia da ke arewacin Gaza bayan harin da Isra’ila ta kai kan rukunin gidaje akalla 12 a gundumar Nadi Khadamat.

Indonesiya

Shugaban kasar Indonesiya Joko Widodo ya bukaci Biden da ya taimaka wajen dakatar da kisan gilla da Isra’ila ke yi a Gaza.

Wasu 'yan kasar Indonesiya sun fara kauracewa kasuwancin Amurka ciki har da McDonald's bayan da kamfanin samar da abinci na Isra'ila ya sanar da cewa ya ba da gudummawar abinci ga sojojin Isra'ila.

Shugaban kasar Indonesia Joko Widodo yayin ganawa da takwatansa na Amurka Joe Biden.13/11/23
Shugaban kasar Indonesia Joko Widodo yayin ganawa da takwatansa na Amurka Joe Biden.13/11/23 AP - Andrew Harnik

Kauracewan na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban kasar Indonesiya Joko Widodo ke Amurka inda zai halarci taron kungiyar APEC a San Francisco.

A ranar Litinin Widodo ya ce "tsagaita bude wuta ya zama tilas don kare bil'adama" kuma ya kamata Amurka "ta kara yin kokarin dakatar da ayyukan cin zarafi a Gaza".

Brazil

Shugaban kasar Brazil Luiz Inacio Lula da Silva ya yi Allah wadai da kisan mata da kananan yara da Isra’ilan ke yi a zirin Gaza.

Wasu 'yan kasar Brazil da ke barin yankin Gaza.13/11/23
Wasu 'yan kasar Brazil da ke barin yankin Gaza.13/11/23 REUTERS - UESLEI MARCELINO

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.