Isa ga babban shafi

Mutanen da aka kora daga Gaza na fama da kura,sanyi da yunwa

Dubban mazauna yankin Gaza ne suka yi imani cewa yaƙi da Isra’ila zai ƙare da sauri. Sai dai dama sun fuskanci fushin Isra’ila,wanda ya kai wasu ga rasa gidajensu,yayinda wasu suka rasa ‘yan uwansu.Dubban mutane, suka fice zuwa kudancin zirin Gaza.

Rayuwa a yankin Gaza yan lokuta bayan hare-haren Isra'ila
Rayuwa a yankin Gaza yan lokuta bayan hare-haren Isra'ila © ISMAIL ZANOUN / AFP
Talla

Falasdinawa da dama suka fice daga gidajensu ,wasu a zaune a kan manyan motoci, wasu saman jakuna ko kuma a kafa, dubban Falasdinawa ne ke tserewa hare-haren Isra’ila.

A cikin kwanaki uku, kusan mutane 200,000 ne suka bar arewacin zirin Gaza zuwa kudanci

Kasashe da dama ne suka bayyana damuwa ganin ta yada Falesdinawa ke rayuwa,daruruwan iyalai suna jiran ruwa ko abinci. Yara da dama zaune a kasa ko suna barci a kafadar iyaye.

Wasu alkaluma na nuni cewa kusan gida daya cikin biyu ya lalace a yankin na Falasdinu da a yanzu ke da sama da mutane miliyan daya da rabi da muhallansu, a wani rahoton Majalisar Dimkin Duniya.

Al'umar Gaza na tserewa daga hare-haren Isra'ila
Al'umar Gaza na tserewa daga hare-haren Isra'ila AP - Fatima Shbair

Wata mata daga Gaza ta sheidawa kamfanin Dillanci labaren Faransa  cewa ‘ba ta da biredi da za ta iya  ciyar da iyalanta.

 Wannan mata ta isa Khan Younès kwanaki uku da suka wuce tare da mijinta da 'ya'yanta bakwai.

Mutanen yankin Gaza cilkin jimami
Mutanen yankin Gaza cilkin jimami AFP - MOHAMMED ABED

A ranar 7 ga watan Oktoba, kungiyar Hamas mai iko a Gaza, ta kaddamar da wani hari da ba a taba gani ba a Isra'ila, inda ta kashe mutane 1,200, galibi fararen hula, tare da yin garkuwa da sama da mutane 240, a cewar hukumomin Isra'ila. Tun a wancan lokaci Isra'ila ta ci gaba da kai hare-hare a zirin Gaza, inda ta kashe mutane fiye da 11,000, musamman fararen hula, a cewar ma'aikatar lafiya ta Hamas.

Hari Isra'ila a yankin Gaza
Hari Isra'ila a yankin Gaza REUTERS - Evelyn Hockstein

Tuni kafin wannan rikici, kusan kashi 80% na Falasdinawa ke  rayuwa cikin talauci kuma kusan kashi biyu cikin uku sun dogara da taimakon kasa da kasa, a cewar Majalisar Dinkin Duniya. A yau, da hauhawar farashin fulawa, abin ya fi muni. Amma yunwa ba ita ce kawai damuwar mtanen Gaza.Mutane na barci a kasa, a cikin ƙura kuma ba su da bargo duk da cewa da dare ana sanyi sosai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.