Isa ga babban shafi

Marasa lafiya na cikin mawuyacin hali a Gaza

Bangaren kiwon lafiya a Zirin Gaza na fuskantar gagarumar barazana, a daidai lokacin da alkaluma ke nuna cewa, akwai kimanin mutane dubu 30 da ke fama da mabanbantan raunuka a sanadiyar hare-haren Isra’ila.

Asibitocin Gaza na cikin mawuyacin hali
Asibitocin Gaza na cikin mawuyacin hali AP - Hatem Moussa
Talla

Yanzu haka Hukumar Lafiya ta Duniya WHO na fafutukar ganin an fitar da mutanen da rashin lafiyarsu ta tsananta matuka zuwa wasu kasashen ketare daga Gaza domin ci gaba jinya.

Tuni kasashe irinsu Masar da Turkiya da Hadaddiyar Daular Larabawa suka amince su karbi wasu daga cikin wadannan marasa lafiya da ke cikin mawuyacin hali.

Da ma dai gabanin barkewar yakin na Gaza, akwai kimanin mutane dubu 20 da ke neman izini daga Isra’ila don fita duba lafiyarsu a kowacce shekara, kuma kusan kashi daya bisa uku kananan yara ne.

A bara kadai, Isra’ila ta amince da kashi 63 cikin 100 na marasa lafiyar da su fice daga Gaza don ketara iyaka da zummar duba lafiyarsu.

A halin yanzu, akwai mutane dubu 350 da ke fama da miyagun cututtuka a Gaza da suka hada da ciwon siga da kansa, yayin da ake da mata dubu 50 masu juna biyu kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana.

Wannan dai ya dada fito da halin da bangaren kiwon lafiya ke ciki ne a Gaza gabanin yakin da ya barke a baya-bayan nan, inda babu shakka lamarin ya kara kazancewa a yanzu da ake da dimbin majinyata da suka samu raunuka.

Jami’an kiwon lafiya sun yi gargadin cewa, akwai yiwuwar samun tarin mutane da za su mutu a Gaza saboda rashin kula da lafiyarsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.