Isa ga babban shafi

IS ta ce an kashe shugabanta Abu Hassan al-Quraishi

Kungiyar IS, mai ikirarin jihadi ta ce an kashe shugabanta,  Abu Hasan al-Hashimi al-Qurashi ayayin wani gumurzu, kuma har ta sanar da wanda zai maye gurbinsa.

is ta sanar da mutuwar shugabanta Abu Hassan al-Quraishi.
is ta sanar da mutuwar shugabanta Abu Hassan al-Quraishi. REUTERS/Stringer
Talla

Wani kakakin kungiyar, ya ce wau maakiya Allah ne suka kashe Hashimi, wanda dan kasar Iraqi ne, amma bai yi wani karin bayani a game da rana ko yadda aka kashe shi ba.

Rundunar sojin Amurka ta CENTCOM ta ce ‘yan tawayen Syria ne suka kashe Hashimi a wani samame da suka kai lardin Daraa a kudancin Kasara. tsakiyar watan Oktoba.

Akasarin lardin Daraa yana karkashin dakarun gwamnatin Syria da ‘yan tawaye da suka cimma jituwa da mahukuntan kasar ne. Kuma a tsakiyar watan Oktoba, gwamnatin ta ce ta kaddamar da wani samame na hadin gwiwa a kan kungiyar IS a kudancin kasar.

Kakakin mjalisar tsaron Amurka, John Kirby ya ce ji dadin samun labarin cewa yanzu sshugaban IS  ba ya taiya a doron kasa.

A wani sakon urya da aka watsa, kakakin IS din ya ce an bayyana Abu al-Hussein al-Husseini al-Qurashi a matsayn sabon sshugaban kungiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.