Takunkumin da Saudiya ta laftawa Lebanon ya jefa ta cikin tasku
Kusan makwanni biyu kenan da Saudiyya ta haramta da shigar da kayayyaki daga Lebanon zuwa cikinta, bayan da wani karamin ministan kasar ta Labanon ya caccaki masarautar kan yakin da take jagoranta a kasar Yemen, inda take gwabzawa da mayakan ‘yan tawayen Houthi dake samun goyon bayan Iran.
Wallafawa ranar:
Yanzu haka dai takunkumin da Saudiya ta laftawa Lebanon ya sake jefa kasar cikin mawuyacin hali, wadda dama ke fama da matsalar durkushewar tattalin arzikin da kwararru suka bayyana a matsayin mafi muni a duniya cikin shekarun baya bayan nan.
Wani mamba a kungiyar masu masana'antu ta kasar Lebanon Paul Abi Nasr, ya ce a halin da ake ciki, tuni matakin Saudiya ya janyo musu tafka hasarar kusan dala miliyan 250 a bangaren fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje.
Tattalin arzikin Lebanon dai na ci gaba da nutsawa cikin mawuyacin hali, durkushewar da ya fara tun a shekarar 2019.
Cikin shekaru biyu da suka gabata, kudin kasar Lebanon na fam ya yi asarar kusan kashi 90 cikin dari na darajarsa, zalika kusan kashi uku cikin hudu na yawan al'ummar kasar na rayuwa cikin talauci.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu