Isa ga babban shafi
Lebanon

Kotu ta hana fallasa rahoton tashin bama-bamai a Beirut

Wata kotu a Lebanon ta dakatar da jagoran tawagar masu gudanar da bincike kan musababbin tashin bama-bamai a tashar jiragen ruwan birnin Beirut a bara daga gabatar da rahotonsa.

Sama da mutane 200 suka rasa rayukansu, sannan gine-gine masu tarin yawa suka rushe a sanadiyar tashhin bam din.
Sama da mutane 200 suka rasa rayukansu, sannan gine-gine masu tarin yawa suka rushe a sanadiyar tashhin bam din. AFP
Talla

Bayanai sun ce, kotun ta dauki wannan mataki ne bayan guda daga cikin ministocin da masu gabatar da binciken suka bukaci ya yi musu bayani, shi kuma ya yi musu tirjiya tare ma da gurfanar da su a gaban kotu yana bukatar a sauya masu gudanar da binciken musamman jagoransu Tarek Bitar.

Wannan na nufin cewa jagoran masu gudanar da binciken da Tarek Bitar zai dakatar da ci gaba da binciken da kuma gabatar da rahoton binciken da ya gudanar a baya, har sai zuwa lokacin da kotu ta kamalla sauraren karar da ministan harkokin cikin gidan kasar Nohad Machnouk ya gabatar mata na bukatar a sauyan jagoran masu gudanar da binciken.

Machnok dai na cikin na gaba-gaba da ake zargin suna da ruwa da tsaki wajen tayar da bam din da ya yi sanadiyyar hallaka mutane sama da 200 a ranar 4 ga watan Agustan bara.

Wannan ne dai karo na biyu da ake dakatar da binicken, kuma idan kotu ta yanke hukuncin cire Bitar daga cikin masu gudanar da binciken, to zai zama mutum na biyu da aka cire daga jagorantar binciken tashin bam din da ake ganin akwai sa hannun ‘yan siyasar Lebanon a ciki.

Kafin Tarek Bitar, Fadi Sawan shi ne jagoran tawagar masu gudanar da binciken, kuma a watan Fabrairun bana ne wasu ministocin kasar suka bukaci kotu ta dakatar da shi daga ci gaba da gudanar da binciken tare da sauya shi da wanin sa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.