Isa ga babban shafi
Lebanon

Zanga-zanagr Lebanon ta koma rikici tare da kashe akalla mutum 6

Akalla mutane 6 suka mutu a kasar Lebanon yayin da wasu 30 suka jikkata sakamakon bude wuta a zanga-zangar-zangar da Kungiyoyin Shi’a ta Hizbollah da Amal suka shirya a wannan Alhamis inda suke neman a kori  babban mai binciken fashewar tashar jiragen ruwan Beitut na bara.

Dakarun Lebanon da aka baza yankin mai tarzoma a Beirut 14/10/21.
Dakarun Lebanon da aka baza yankin mai tarzoma a Beirut 14/10/21. Joseph Eid AFP
Talla

Tun farko Mariam Hassan na Asibitin Sahel galibi na ‘yan shi’a dake kuduncin Beirut tace mutum daya ya mutu sakamakon harbin bindiga a kai sai kuma na biyu da aka harba a kirji.

Likitan ta kara da cewa wata mata 'yar shekara 24 ta mutu a gidanta bayan harsashi ya riske ta.

Kamfanin dillancin labarai na gwamnati ya ba da rahoton mutuwar mutun na hudu a asibitin Rasoul al-Azam, shi ma a kudancin kasar.

Kungiyar agaji ta Red Cross dake Lebanon ta ce mutane 20 sun jikkata, yayin da Wakilan kamfanin dillancin labarai na AFP a yankin suka tabbatar da jin karar harbe -harbe.

Gidan talabijin na Lebanon ya watsa hotunan mutanen dauke da bindigogi da manyan makamai.

A wata sanarwa da rundunar sojin kasar ta fitar, ta yi gargadin cewa za ta bude wuta kan duk wanda aka gani yana harbi, tare da yin kira ga fararen hula da su kaurace wa yankin.

Firayinminista Najib Mikati ya yi kira da a kwantar da hankula tare da gargadi kan yunkurin sanya kasar ta Lebanon cikin tashin hankali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.