Isa ga babban shafi

Fashewar tankar mai a Lebanon ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 28

Wata fashewar tankar mai da ta faru a kasar Lebanon ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 28 tare da jikkata sama da 80.Wannan dai ya tayar da hankalin mutanen kasar, la’akari da yadda al’amarin ya shafi mutane da dama.

Wasu daga cikin wurrare da aka fuskanci barnar wuta a Lebanon
Wasu daga cikin wurrare da aka fuskanci barnar wuta a Lebanon Joseph Eid AFP
Talla

Rahotanni sun bayyana cewa tun da fari fashewar ta faru ne a wani gidan mai, wanda ke cike da mutane a kan layin sayan man fetur saboda karancin sa a kasar.

Gobarar da ta tashi a kasar Lebanon
Gobarar da ta tashi a kasar Lebanon AFP - GHASSAN SWEIDAN

Jami’an lafiya a kasar sun bayyana cewa ya zuwa yanzu ana ci gaba da kai wadanda fashewar tankar man ta shafa zuwa asibitoci, a kasar mai fama da rikice-rikice.

Lamarin da ya faru da daddare a arewacin kasar ya tashi hankalin jama’a a kasar da ke fama da matsin tattalin arziki da karancin man fetur, abinda ya durkusar da harkokin kiwon lafiya kwarai da gaske.

Fashewar tankar man ta tunawa jama’ar kasar tashi bama baman da aka samu a Birnin Beirut a watan Agustan bara, da ya hallaka mutane sama da 200 da kuma lalata dukiyoyi masu tarin yawa.

Jami'an kwana -kwana na kokarin kashe wuta
Jami'an kwana -kwana na kokarin kashe wuta via REUTERS - TWITTER/ @LEXI_BELLSY

A cewar mai baiwa ministan harkokin lafiyar kasar shawara adadin wadanda suka mutu sanadiyyar fahsewar tankar da aka samu a kauyen Al-Tleil da ke gundumar Akkar ka iya karuwa, saboda yawan wadanda suka jikkata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.