Isa ga babban shafi
Lebanon

Lebanon ta kafa sabuwar gwamnati bayan watanni 13

Lebanon ta kawo karshen zaman jiran watanni 13 ta na dakon kafa sabuwar gwamnatin da za ta kagoranci kasar, inda a yau Juma’a fadar shugaban kasa ta kaddamar da Majalisar Ministocin da alhakin ceto kasar daga tabarbarewar tattalin arziki.

Shugaba Michel Aoun da Firaminista Najib Mikati.
Shugaba Michel Aoun da Firaminista Najib Mikati. STRINGER DALATI AND NOHRA/AFP
Talla

Sanarwar kafa sabuwar gwamnatinya biyo bayan ganawa tsakanin Firaminista Najib Mikati da shugaba Michel Aoun, bayan musayar yawun da aka samu tsakanin manyan bangarorin  ‘yan adawar siyasar kasar na ‘yan watanni.

Cikin wata tattauna wa da aka samu a fadar shugaban kasar tsakanin Firaminista Mikati da  Michel Aoun ya biyo bayan watannin da aka kwashe ana raba mukamai tsakanin bangarorin siyasar kasar.

Mikati ya ce za su yi amfani da duk wata dama da su ke da ita wajen jawo hankalin duk wasu hukumomi na kasashen waje don tabbatar da ganin ana samun cimma bukatu na yau da kullum.

Mikati da aka nada shi mukamin Firaminista a watan Yulin da ya gabata bayan gazawar wasu magabatan sa har su biyu bisa rashin cimma yarjejeniyar wasu batutuwa da aka shirya tuni ya bayyana jerin ministocin da zai yi aiki da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.